Skip to content
Habakkuk 3:16-19

Habakkuk 3:16-19

16
Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
17
Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,
18
duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.
19
Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options