Farawa 7:10-12
10
Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.
11
A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
12
Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
Settings