Farawa 40:8-19
8
Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.” Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.”
9
Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana,
10
kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi.
11
Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.”
12
Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne.
13
Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
14
Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku.
15
Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’ ”
16
Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi.
17
A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.”
18
Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne.
19
Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”
Settings