Farawa 1:9-13
9
Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
10
Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
11
Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
12
Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.
13
Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
Settings