Ezra 6:16-22
16
Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki.
17
Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila.
18
Suka kuma naɗa firistoci a gundumominsu da kuma Lawiyawa a ƙungiyoyinsu don hidimar Allah a Urushalima, bisa ga abin da aka rubuta a Littafin Musa.
19
A rana ta goma sha huɗu ga watan farko, sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi Bikin Ƙetarewa.
20
Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin ’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu.
21
Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
22
Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila.
Settings