Skip to content
Ezra 10:1-4

Ezra 10:1-4

1
Yayinda Ezra yake addu’a, yake kuma furta laifi, yana kuka, yana a durƙushe da kansa ƙasa a gaban gidan Allah, sai babban taron jama’ar Isra’ilawa, maza, mata da yara, suka taru a wurinsa. Su ma suka yi kuka mai zafi.
2
Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba.
3
Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka.
4
Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options