Skip to content
Ezekiyel 5:8-12

Ezekiyel 5:8-12

8
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai.
9
Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba.
10
Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska.
11
Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba.
12
Kashi ɗaya bisa uku na mutanenki za su mutu da annoba ko su mutu da yunwa a cikinki; kashi ɗaya bisa uku takobi ne zai kashe su a waje da katangarki; kashi ɗaya bisa uku kuma zan watsar a iska in kuma fafare su da takobin da aka zāre.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options