Ezekiyel 39:9-16
9
“ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta.
10
Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
11
“ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.
12
“ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar.
13
Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
14
“ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu.
15
Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog.
16
Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’
Settings