Skip to content
Ezekiyel 38:18-23

Ezekiyel 38:18-23

18
Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
19
Cikin kishina da hasalata mai zafi zan furta cewa a wannan lokaci za a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra’ila.
20
Kifin teku, tsuntsayen sarari, namun jeji, kowace halitta mai rarrafe da kuma dukan mutane a duniya za su yi rawar jiki a gabana. Za a tumɓuke duwatsu, a ragargaza tsaunuka, kuma kowane bango zai fāɗi ƙasa.
21
Zan kira takobi a kan Gog a dukan duwatsuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Kowane takobin mutum zai yi gāba da ɗan’uwansa.
22
Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi.
23
Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options