Ezekiyel 32:17
Ana nuna aya 17 tare da mahallin da ke kewaye.
14
Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta in sa rafuffukanta su gudu kamar mai, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15
Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’
16
“Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
17
A shekara ta goma sha biyu, a rana ta goma sha biyar ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
18
“Ɗan mutum, yi kuka saboda jama’ar Masar ka kuma tura ta da ’yan matan manyan al’ummai zuwa ƙarƙashin ƙasa, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
19
Ka ce, ‘Kin fi sauran tagomashi ne? Ki gangara, ki kwanta cikin marasa kaciya.’
20
Za su fāɗi cikin waɗanda aka kashe da takobi. Takobin da an zāre; bari a ja ta a tafi tare da dukan jama’arta.
Settings