Skip to content
Ezekiyel 29:1-9

Ezekiyel 29:1-9

1
A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3
Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar, kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka. Ka ce, “Nilu nawa ne; na yi shi wa kaina.”
4
Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka. Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka, da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
5
Zan bar ka a cikin hamada, kai da dukan kifin rafuffukanka. Za ka fāɗi a fili ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba. Zan ba da kai kamar abinci ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama.
6
Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila.
7
Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.
8
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi.
9
Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options