Skip to content
Ezekiyel 28:24-26

Ezekiyel 28:24-26

24
“ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
25
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub.
26
Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options