Skip to content
Ezekiyel 28:6-10

Ezekiyel 28:6-10

6
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah,
7
zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.
8
Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna.
9
Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,” a gaban waɗanda suka kashe ka? Za ka zama mutum kurum, ba allah ba, a hannuwan waɗanda suka kashe ka.
10
Za ka yi mutuwar marar kaciya a hannuwan baƙi. Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options