Ezekiyel 28:11-19
11
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
12
“Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau.
13
Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.
14
An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
15
Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka.
16
Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.
17
Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.
18
Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.
19
Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Settings