Skip to content
Ezekiyel 28:21-23

Ezekiyel 28:21-23

21
“Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta
22
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon, zan sami ɗaukaka a cikinki. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na zartar da hukunci a kanta na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.
23
Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options