Ezekiyel 25:8-11
8
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,”
9
saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar.
10
Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai;
11
zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Settings