Ezekiyel 25:15-17
15
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda,
16
saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku.
17
Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ”
Settings