Ezekiyel 12:1-7
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
2
ɗan mutum, kana zama a cikin mutane masu tawaye, Suna da idanun gani amma ba sa gani, suna da kunnuwan ji amma ba sa ji, gama ’yan tawaye ne.
3
“Saboda haka ɗan mutum, ka tattara kayanka don zuwa zaman bauta, ka tashi da rana suna gani ka ƙaura a inda kake zuwa wani wuri. Mai yiwuwa za su gane, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.
4
Da rana, yayinda suke kallo, ka fid da kayanka da ka tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma, yayinda suke kallo, ka fita kamar yadda mutane masu tafiyar zaman bauta sukan yi.
5
Yayinda suke kallo, ka huda katanga ka fitar da kayanka daga ciki.
6
Ka sa su a kafaɗarka yayinda suke kallo ka kuma fitar da su da dare. Ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na mai da kai alama ga gidan Isra’ila.”
7
Sai na yi kamar yadda aka umarce ni. Da rana na fitar da kayana da na tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma na huda katanga da hannuwana. Na kwashe kayana da dare, na ɗauke su a kafaɗuna yayinda suke kallo.
Settings