Ezekiyel 11:1-12
1
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a.
2
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta suna kuma ba da muguwa shawara a cikin wannan birni.
3
Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’
4
Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.”
5
Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku.
6
Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki.
7
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta.
8
Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9
Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku.
10
Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
11
Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila.
12
Za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji, gama ba ku bi ƙa’idodina ba balle ku kiyaye dokokina, amma kuka bi hanyoyin al’ummai kewaye da ku.”
Settings