Fitowa 7:7-12
7
Musa yana da shekara tamanin da haihuwa, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku, sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.
8
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
9
“Sa’ad da Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata wani al’ajabi,’ sai ka ce wa Haruna, ‘Ɗauki sandanka ka jefa shi a ƙasa, a gaban Fir’auna,’ zai kuwa zama maciji.”
10
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji.
11
Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu.
12
Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.
Settings