Fitowa 39:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
2
Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin.
3
Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.
4
Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa.
Settings