Skip to content
Fitowa 32:1-8

Fitowa 32:1-8

1
Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.”
2
Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.”
3
Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna.
4
Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”
5
Da Haruna ya ga haka, sai ya gina bagade a gaban ɗan maraƙi, ya yi shela ya ce, “Gobe akwai biki ga Ubangiji.”
6
Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa.
7
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu.
8
Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options