Skip to content
Fitowa 31:1-11

Fitowa 31:1-11

1
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,
3
na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a,
4
don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla,
5
don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.
6
Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.
7
Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin,
8
tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare,
9
bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa,
10
da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci,
11
da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options