Afisawa 3:1-7
1
Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.
2
Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.
3
Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri.
4
A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi.
5
Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa.
6
Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.
7
Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.
Settings