Mai Hadishi 2:1-11
1
Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani.
2
Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?”
3
Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.
4
Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi.
5
Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu.
6
Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa.
7
Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni.
8
Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
9
Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba.
10
Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.
11
Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya.
Settings