Mai Hadishi 10:4-7
4
In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
5
Akwai muguntar da na gani a duniya, irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.
6
Akan sa wawaye a manyan matsayi, yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.
7
Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, yayinda ’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.
Settings