Skip to content
Mai Hadishi 1:2-11

Mai Hadishi 1:2-11

2
“Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!”
3
Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya?
4
Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada.
5
Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6
Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7
Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.
8
Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9
Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance, abin da aka yi za a sāke yi kuma; babu wani abu sabo a duniya.
10
Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu.
11
Ba a tunawa da mutanen dā, haka su ma da ba a haifa ba tukuna waɗanda za su biyo bayansu ba za a tuna da su ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options