Maimaitawar Shari’a 7:13-14
13
Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku.
14
Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa.
Settings