Maimaitawar Shari’a 6:7-9
7
Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
8
Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.
9
Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.