Maimaitawar Shari’a 4:9-10
9
Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.
10
Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”
Settings