Maimaitawar Shari’a 33:2-4
2
Ya ce, “Ubangiji ya zo daga Sinai ya haskaka a bisansu daga Seyir; ya haskaka daga Dutsen Faran. Ya zo tare da dubban tsarkakansa daga kudu, daga gangara dutsensa.
3
Tabbatacce kai ne wanda yake ƙaunar mutane; dukan tsarkaka suna a hannunka. A ƙafafunka, duk suka rusuna, daga wurinka kuma suka karɓi umarni,
4
dokar Musa ta ba mu dokoki, mallakar taron Yaƙub.
Settings