Maimaitawar Shari’a 30:15-16
15
Ku duba, na sa a gabanku a yau, rai da wadata, mutuwa da kuma hallaka.
16
Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.
Settings