Maimaitawar Shari’a 24:16
Ana nuna aya 16 tare da mahallin da ke kewaye.
13
Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku.
14
Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.
15
Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.
16
Ba za a kashe iyaye a maimakon ’ya’yansu ba, ba kuwa za a kashe ’ya’ya a maimakon iyayensu ba; kowa ya yi zunubi, shi za a kashe.
17
Ba za ku danne hakkin baƙon da yake zama a cikinku ko na marayu ba, ba za ku ɗauki rigar matar da mijinta ya mutu a matsayin jingina ba.
18
Ku tuna dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuwa ya fisshe daga can. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan.
19
Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.
Settings