Maimaitawar Shari’a 23:1-8
1
Duk wanda aka daƙe, ko yanke gabansa, ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
2
Duk wanda aka haifa ta wurin cikin shege, har tsara ta goma, zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba, har zuwa tsara ta goma.
3
Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma.
4
Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku.
5
Amma Ubangiji Allahnku bai saurari Bala’am ba, sai ya mai da la’anar ta koma albarka gare ku, domin Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.
6
Kada ku yi yarjejjeniyar abuta da su, muddin kuna da rai.
7
Kada ku yi ƙyamar mutumin Edom, gama mutumin Edom ɗan’uwanku ne. Kada ku yi ƙyamar mutumin Masar, domin kun yi zama baƙunta a ƙasarsa.
8
’Ya’yan da aka haifa musu na tsara ta uku za su iya shiga taron jama’ar Ubangiji.
Settings