Maimaitawar Shari’a 18:18-22
18
Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi.
19
Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin.
20
Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”
21
Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?”
22
In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.
Settings