Maimaitawar Shari’a 18:15-19
15
Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi.
16
Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.”
17
Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau.
18
Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi.
19
Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin.
Settings