Maimaitawar Shari’a 13:12-17
12
In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki
13
cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba),
14
to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku,
15
dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa.
16
Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi.
17
Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku,
Settings