Maimaitawar Shari’a 11:2-5
2
Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;
3
alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;
4
ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.
5
Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,
Settings