Skip to content
Maimaitawar Shari’a 1:26-36

Maimaitawar Shari’a 1:26-36

26
Amma ba ku yi niyya ku haura ba, kuka yi tawaye gāba da umarnin Ubangiji Allahnku.
27
Kuka yi gunaguni a cikin tentunanku, kuna cewa, “Ubangiji ya ƙi mu; shi ya sa ya fitar da mu daga Masar don yă ba da mu ga hannuwan Amoriyawa su hallaka mu.
28
Ina za mu? ’Yan’uwanmu suka sa muka fid da zuciya. Suka ce, ‘Mutanen sun fi mu ƙarfi, sun kuma fi mu tsayi; biranen manya ne, da katanga har sama. Mun ma ga Anakawa a can.’ ”
29
Sai na ce muku, “Kada ku firgita; kada ku ji tsoronsu.
30
Ubangiji Allahnku yana a gabanku, zai yi yaƙi saboda ku, kamar yadda ya yi a kan idanunku a Masar,
31
da kuma a cikin hamada. A can ma kun ga yadda Ubangiji Allahnku ya riƙe ku ko’ina da kuka tafi, kamar yadda mahaifi yakan riƙe ɗansa, sai da kuka kai wannan wuri.”
32
Duk da haka, ba ku amince da Ubangiji Allahnku ba,
33
shi da ya sha gabanku a tafiyarku, cikin wuta da dad dare da kuma girgije da rana, don yă nemi wurare domin ku kafa sansani, don kuma yă nuna muku hanyar da za ku bi.
34
Da Ubangiji ya ji abin da kuka faɗa, sai ya husata, ya kuma yi rantsuwa ya ce,
35
“Babu wani a cikin wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba wa kakanninku,
36
sai dai Kaleb ɗan Yefunne. Zai gan ta, zan ba shi duk ƙasar da tafin ƙafarsa ta taka, shi da zuriyarsa, gama ya bi Ubangiji da zuciya ɗaya.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options