Daniyel 9:5-8
5
mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.
6
Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.
7
“Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.
8
Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.
Settings