Skip to content
Daniyel 7:28

Daniyel 7:28

Ana nuna aya 28 tare da mahallin da ke kewaye.
25
Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.
26
“ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.
27
Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’
28
“Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options