Kolossiyawa 4:15-18
15
Ku miƙa gaisuwata ga ’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.
16
Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.
17
Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.
18
Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku.
Settings