Amos 9:5-8
5
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke, kuma dukan mazauna cikinta suna makoki, ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu, sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,
6
shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai ya kuma kafa harsashenta a duniya, shi da yakan kira ruwan teku yă kuma kwarara su a bisa duniya, Ubangiji ne sunansa.
7
“Ku ba Isra’ilawa ba ne, daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?” In ji Ubangiji. “Ban fito da Isra’ila daga Masar ba, Filistiyawa kuma daga Kaftor Arameyawa kuma daga Kir ba?
8
“Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka suna a kan mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka shi daga fuskar duniya, duk da haka ba zan hallaka gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.
Settings