Skip to content
Ayyukan Manzanni 8:32-35

Ayyukan Manzanni 8:32-35

32
Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.
33
A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”
34
Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?”
35
Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options