Ayyukan Manzanni 5:21-24
21
Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.
22
Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce,
23
“Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.”
24
Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.
Settings