Skip to content
Ayyukan Manzanni 3:16-26

Ayyukan Manzanni 3:16-26

16
Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.
17
“To, ’yan’uwa, na san cewa, kun aikata wannan cikin jahilci ne, yadda shugabanninku suka yi.
18
Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala.
19
Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,
20
don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan.
21
Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.
22
Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku.
23
Duk wanda bai saurare shi ba za a ware shi gaba ɗaya daga mutanensa.’
24
“Tabbatacce, dukan annabawa daga Sama’ila zuwa gaba, dukansu da suka yi magana, sun rigya faɗin waɗannan kwanaki.
25
Ku kuwa magādan annabawan ne da kuma na alkawarin da Allah ya yi da kakanninku. Ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilan duniya za su sami albarka.’
26
Da Allah ya tashe bawansa, ya aike shi da fari zuwa gare ku don yă albarkace ku ta wurin juye kowannenku daga mugayen hanyoyinku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options