Ayyukan Manzanni 26:4-11
4
“Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima.
5
Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne.
6
Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau.
7
Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena.
8
Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu?
9
“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.
10
Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su.
11
Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.
Settings