Ayyukan Manzanni 24:24-27
24
Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
25
Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.”
26
A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
27
Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.
Settings