Skip to content
Ayyukan Manzanni 22:17-21

Ayyukan Manzanni 22:17-21

17
“Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi
18
na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’
19
“Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka.
20
Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’
21
“Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options