Ayyukan Manzanni 14:21-25
21
Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,
22
suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
23
Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
24
Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya,
25
kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.
Settings